Shugabannin kasashen Afirka na cigaba da zargin kotun da yi wa shugabannin nahiyar bi-ta-da-kulli, inda suka fi son a kafa wata kotu ta musamman a nahiyar wadda za ta dinga hukunta tauyen hakkin bil'adama.
Taron na kwana biyu zai kuma tattauna a kan rikicin Sudan ta kudu, da kuma shirin kungiyar Tarayyar Afirka na yin Fasfo na bai-daya.
A wani labarin kuma, Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce Salva Kiir da Riek Machar sun ci amanar al’ummarsu.
Ban da a halin yanzu ke Kigalin kasar Rwanda, domin halartar taron AU karo na 27, ya bukaci Salva Kiir, da mataimakinsa Rick Machar dasu yi aiki domin al’umma.